ClassiQ Na Shirye-Shiryen Saka Gasa Mai Suna ‘New North’

Up North Recordz suna farin ciki sanar da ku
sabon gasar da classik zai saka wanda ba’a
taba yin irinsa arewa ba, mai taken “New
North”.
Gasar New North din ana shirin gabatar da shi
ne a harabar jami’o’in dake Arewa cikin
wannan watan da muke Nuwamba.
Gasar tana cike da tarin abubuwan kayatarwa
kamar wasannin barkwanci kyaututtuka ga
wandanda allah yaba ma sa’a zasu ci.
Daga cikin manyan mawakan da aka gayyata
ya hada da irinsu Jesse Jagz, Ruby Gyang,
CKay, Kheengz, Lyrical Dr Smith, BOC Madaki,
da dai sauransu.
Jadawalin farko na garuruwan da za’a gabatar
da wasan ya hada da Plateau ranar 6th ga
watan Nuwanba da 8th, Nasarawa 10th ga
wata, Abuja 13th ga wata, Kano 15th ga wata,
Borno 17th ga wata, sai Adamawa 20th da 21st
ga wata.
Ka’idojin shiga Gasar:
Ga masu sha’awar shiga gasar zaku iya sauke
App din ALAT a google play ko a Apple Store.
Bayan ka sauke sai kayi Rijista.
Kana da damar da zaka iya cin kyauta har na
10,000 in kasa 1000 kacal a cikin a asusunka
na ALAT din.
Dan haka mai kake jira? Hanzarta ka sauke
App din dan kasancewa tare da gwarzon
mawakin Arewa, Classik mai taken AREWA
MAFIA.

Post a Comment